Yadda zaka kirkiri Facebook account cikin sauki

Akwai masu tambayar yadda ake kirkiran account na Facebook, cikin yaddan Allah yau na samu daman rubutu a kan Wannan matsalar ta kirkiran account din Facebook cikin sauki kuma a kyauta.

Kafin Facebook ya yawaita a duniya an yi lokacin da idan kana bukata a bude maka account a Facebook sai ka biya saboda rashin isassun jama'a masu amfani dashi, ko da yake ta yiwu har a yanzu a iya samun irin haka a wasu guraren domin akwai wadanda basu iya budewa ba kuma ba lallai bane a bude musu Facebook a kyauta.

Kafin ka fara bude Facebook account dole ne a kalla ka kai shekara sha uku (13) a duniya, Wannan na daga cikin dokoki da ka'idodin da Facebook ta bayar ga masu fara tunanin bude account dasu.

Don kirkiran Facebook account:

Da farko zaka shiga 'Create account' Rubuta sunan da kake so ya kasance na account din kaZaka rubuta kwanan wata na ranar haihuwar Ka (Date of birth)Sai ka rubuta lamban wayar ka.

Idan kuma da email za kayi amfani sai ka shiga Sign up with email.Ka zabi gender, idan Kai na Miji ne ka zabi male, Idan Kuma mace ce ke sai ki zabi female.Zabi password kayi sign up.

Don karasa kirkiran account din ka sai ka tabbatar da email ko lamban wayar da ka bude account din dashi.

Idan kana samun matsala da password ko ka manta shi, Shiga nan ka koyi Yadda ake chanja password na Facebook accountFacebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOKWhatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPPTwitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTERInstagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAMCall & Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post