[Phone] Yadda waya take tura sakon kira zuwa wata wayar har ayi magana


Wayar hannu a wannan zamani ta zamo hanya mafi sauki ta sada zumunta, idan kana so kayi magana da wani sai dai ka kira lambarsa nan take kuyi magana. Sai dai har yanzu wasu na mamakin yadda hakan take faruwa.
Bari na dan yi takaitaccen bayani game da kimiyyar fasahar dake tattare a MOBILE COMMUNICATION TECHNOLOGY.
A kowace waya akwai MICROPHONE (Masarrafin daukar magana) akwai INTEGRATED CIRCUIT ( mai chanja magana zuwa lambobi) sannan akwai ANTENNA (Masarrafin dauko magana takai, ko ta dauko)
Kira tsakanin waya da waya yana faruwa ne da taimakon kimiyyar fasahar da ake kira cellular technology.
CELLULAR TECHNOLOGY.
A kimiyyar fasaha ta cellular technology ko wanne yanki ana kafa CELL TOWER (kamar yadda muke ganin kamfani irinsu MTN suna kafa karfen service a kowanne gurin da ake so network ya kai).

YADDA ABIN YAKE.
Yayin da kayi magana akwai wani abu a cikin wayarka mai suna MIC dake daukar maganar ya shigar da shi cikin wayarka, maganar na shiga cikin wayar sai IC ya chanja maimakon sakon murya sai ta koma lambobi shima sai ya turawa ANTENNA itama sai ta chanja lambobin su koma Electrical Magnetic (yana nan kamar hayaki) bayan ta chanja sai ta turawa Cell Tower (Gangar service) shima gangar service (cell tower) sai ya chanja hayakin nan ya koma wani HASKE da ake kira Higher Frequency Light Force, shi kuma wannan hasken sai ya dinga gudu ta karkashin kasa ya kai maganar zuwa wani Cell Tower din wato wani gangar service din dake kusa da wanda ka kira, shi kuma gangar service din sai ya kai wannan hasken zuwa wayar wanda ka kira da hasken ya shiga wayar ta hanyar Antenna sai ya wuce Speaker nan take sai ya ji muryarka radau. Duk wannan yana faruwa ne cikin lokacin da baifi Second daya ba.

Tunda gangar service dinka ke daukar magana ta kai zuwa gangar service din wanda ka kira ita kuma ta tura muryar zuwa wayar wanda ka kira. To ya gangar service naka take gane gangar service din wanda ka kira alhalin ga ganguna nan da yawa kuma kowanne kamfani na da na shi?


Ga yadda abin yake

Kowanne kamfanin NETWORK (irin su MTN, AIRTEL, GLO, ETISALAT, 9JA) yana da wani daki da ake kira MOBILE SWITCHING CENTER (MSC) wannan dakin shine gurin dake kula da kowanne gangar service da wannan kamfanin ke da shi.

Yayin da ka sanya MTN SIM a cikin wayarka, SIM din na dauke da lambobin dakin kula da gangunan service na kamfanin MTN (MTN MSC). A cikin kowanne daki MSC akwai na'urar dake kula da kowanne layi, na'urar na gane lambar MSC din wanda ka kira sannan tana gane wayar dake kashe ko bude.
Yayin da ka kira lambar GLO da layin MTN, wayar ka zata tura Signal zai tafi zuwa gangar service din MTN dake kusa da kai , ita kuma gangar zata tura zuwa dakin MSC na kamfanin network MTN, na'urar dake cikin dakin zata karanta sakon Signal din sai ta gane lambar MSC na layin GLO da ka kira, idan ta gane sai ta tura SIGNAL din zuwa na'urar dakin MSC na kamfanin GLO, idan sakon ya shiga na'urar GLO ita kuma sai ta duba taga ina mai Lamba yake sai ta tura Signal din zuwa gangar service din dake kusa da shi, ita kuma gangar service din ya tura SIGNAL din zuwa wayar wanda ka kira nan take sai yaji Ringing Tone

Lokacin da ka kira wani na san kana jin wata murya na fada maka "The line your are calling is switched off please try again later" idan wayar wanda ka kira tana kashe. Wannan muryar Na'urar dakin MSC na kamfanin layin da ka kira ne, yake fada maka cewa ta bincika Wayar a rufe ya ke.

Post a Comment

Previous Post Next Post