Yadda zaka kirkiri account a Bulk Sms domin yin kasuwanci

Assalamualaikum, barkanmu da warhaka

Kamar dai yanda kuka sani hanyoyi kasuwanci ta internet suna da matukar yawa, idan ma baka sani ba to ka rika kasancewa da wannan shafin insha Allah zamu rika yin posting akansu.

A yaune insha Allahu zamu zo maku da wasu hanyoyi wanda zaka bunkasa kasuwancinka, wato abinda nake nufi zaka iya yin kasuwancinka ta hanyar tura sako da dai sauransu

zamuyi maku bayanin yanda zakayi kasuwancinka ne ta hanyar yin amfani da Bulk Sms

Menene Bulk Sms?

Nasan mutane da yawa zasuyimin wannan tambar, to atakaicen takaitawa dai Bulk Sms wata hanyace da yake baka damar tura sakon Sms sama da dubu goma, sannan kuma duk alokaci daya, Tare da baka damar zaben sunan da kake son ya bayyana a cikin wayar, wanda ka turama wa, amai-makon lambar ka.

Bulk Sms a yau baya da bukatar wata gabatarwa, saboda kasancewar ya zama ruwan dare a cikinmu, Bulk Sms har da ma bankuna sunayin amfani dashi ta wajen abokan huldarsu alert.

Bugu da kari Bulk Sms manyan kamfani da kuma manyan ma'aikatun gwamnati ke turama ma'aikatansu, don gayyatar interviews ko kuma domin meetings da dai sauransu,

Haka zalika da Bulk Sms ne ake amfani dashi wajen tura invitation na daurin aure ko na sa ranar daurin auren, Haka zalika akanyi amfani da Bulk Sms wajen sanar da haihuwa ko kuma sanar da rasuwa, ko kuma duk wasu abubuwa masu muhimmanci da ake so a sanar da mutane.


Tayaya zan bude account a Bulk Sms domin yin kasuwanci na?

To atakaicen takaitawa dai idan kanason ka kir-kiri account a Bulk Sms ba wani abu bane mai wahala, da farko kaje browser din wayarka ka rubuta Www.BulksmsNigeria.com ko kuma ka danna nan kai tsaye da zaran ka shiga zakaga ya kawoka wani shafi kamar hoton dake kasa
Kamar dai yanda kuka gani a hoton dake sama, sai ka danna "Create account, bayan ka danna zakaga ya nuna maka cewa zaka iya yin register da facebook account dinka,  Sannan kuma zaka iya yin register da google account dinka, amma dai kayi amfani da google account dinka wanda yake kan wayarka yafi, saboda duk lokacin da ka tashi shiga cikin account dinka na Bulk Sms, to ba sai kayi sign in ba, kawai kai tsaye zai bude maka, bayan ka danna create account, zakaga ya nuna maka wani shafi kamar haka
Kamar dai yanda kuka gani zakuga nayi amfani da google account dina ne wajen kirkiran account din
Sannan kuma abu na biyu shine wajen sanya lambar waya, shikuma ananne zaka sanya lambar wayar ka, amma idan ka tashi shiga da lambar wayar naka, kada ka sanya sifili na farkon lambar wayar naka, Misali: 9036117711

Da fatan dai am fahimta
Sai kuma abu na uku shine gurin da zaka sanya password dinka, wato duk lokacin da ka tashi shiga cikin account din naka to da wannan password din zaka yi amfani, sai kuma na kasanshi, shikuma ananne zaka mai-maita password din da ka sanya,

Duk bayan ka gama sai ka danna dai-dai gurin da aka rubuta "Update account"

Bayan ka danna zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka:
To a halin yanzu ana da bukatar ka sanya kudi a wallet dinka, saboda ba kyauta bane, dalilin da yasa ma kenan dazaran kayi register to zasu baka kyautar Naira 50.

Dalilin da yasa suke baka kyautar wannan Naira 50 din, saboda da dashine zakayi gwaji, yanda zaka gane ingancin service dinsu,

Wato abinda nake nufi idan ka gwada, sannan kuma ka tura sako, kuma kaga yaje cikin kan-kanin lokaci, kaga ananne zaka tabbatar da cewa service dinsu bashi da wata matsala.

A takaice dai bayan bayan kayi register sun baka Naira 50 din, idan kanason yin gwaji to sai ka danna dai-dai gurin da kukaga na danyi mashi zagaye

Bayan ka danna guri zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka

To yanzu abinda ya rage shine zakayi contacting dinsu ne, shikuma yanda akeyin contacting dinsu shine zakayi verification, shikuma verification anayinsglhi akan Naira dari biyar 500, shikuma wannan Naira 500 din da zaka biyasu, zaka sanya shine a cikin wallet dinka, Sukuma sai su cire #500 din, sai suyi verify dinka, sai kasanya ID dinka, abinda ake nufi da ID shine kamar voters card, ko kuma International passport, Bayan kayi verification zaka iya tura sako a kowani network ba tare da wani matsala ba, Already mun riga mun fada cewa dole sai ka sanya kudi a cikin wallet dinka sannan zaka iya tura messages, Idan har wallet dinka ya kasance babu kudi kudi a cikinsa, to baza ka iya tura sakon ba,

To kamar dai yanda kuka gani a wannan hoton na kasa zakuga inda aka rubuta "Buy Sms Unit"
To sai ka shiga "Buy Sms units" bayan ka shiga zakaga gurin da aka rubuta "Via paystack" sai ka shiga gurin domin biyan kudin ka ta katinka na ATM.

Minimum deposit shine Naira 500, Sannan kuma zaka iya biya ta banki, zasu baka account dinsu na banki da zaka biya kudin ta banki, sai kazo kayi notify ka fada masu cewa ka sanya kudi adadi kaza, sukuma zasu duba, Idan sun ga transaction dinka yayi sai suyi activated su sanya maka unit naka,

Compose Sms

Shikuma compose Sms ananne zaka rubuta sakon (sms)

Schedule Sms

shikuma Schedule Sms kamar misali daurin aure kanaso nan da sati uku ko hudu, to sai ka shiga scedule sms ka tura message din, idan har ka tura to message din bazai taba gogewa ba har sai ya kai iya adadin da ka sanya yayi


Smart Sms

Shikuma Smart Sms wasu sakonni ne wanda suka rubuta da kansu, wanda ba lallai sai ka rubuta da kanka ba, a'a shi wannan kawai a rubuce yake, Misali kamar daurin aure, kawai zaka ganshi ne a rubuce, kawai abinda zakayi shine, zaka sanya kwanan wata ne da kuma lokacin da za'a yi wannan abum


Sannan kuma sai ka danyi kasa kadan zaka gani kamar haka


Post a Comment

Previous Post Next Post