Hanyoyin Kare Lafiyar ka daga cututtukan da amfani waya (phone) ke janyowa || Hausaweb.com.ng

Maraba da sake kasancewa a cikin wannan shafin namu mai albarka,
Kasancewar wayar hannu sun zama wani jigo na rayuwar mu, mutane da yawa ba zasu iya zama babu waya ba koda na kwana daya ne sai fa idan ya zama DOLE.

Karanta Wannan: Abubuwa 3 dayakamata kafara yi Kafin kayi apply na Adsense
Yadda ake siyan Data a layin Airtel cikin Sauki


Bincike ya nuna mutanen wannan karnin ba zasu jima da lafiya ba kamar mutanen da suka rigaye mu sanadiyyar amfani da wayoyin hannu.
Wayar da kake amfani da ita tana da Illa sosai ga lafiyar cikin dan Adam. Mafi yawan cutar Cancer mutane suna samu ne sanadiyyar amfani da WAYA (phone) ba su sani ba.
Ga wasu hanyoyi da zasu taimaka maka ka kare lafiyarka da lafiyar wayar ka.1. Ka nesanta wayar daga jikinka:


Wayoyin hannu an kirkire sune don a rike su a hannu, idan ba ya zama dole ba kada ka sanya waya a Aljihu. Mata suna sanya waya a BRA lokacin da suke aikace-aikacen gida wanda hakan na haifar da Breast cancer. 


Karanta Wannan: Idan na chanja Template Adsense dina zai samu matsala?2. Ka yawaita kashe wayarka:

Kamar yadda mutum ke bukatar bacci domin inganta lafiyarsa itama waya tana bukatar a dinga kashe ta domin tayi Refreshing. 3. Kasanya wayarka (phone)  a flight mood:

Duk lokacin da zaka bawa karamin yaro wayarka ka tabbatar ka sanya wayar flight mood.4. Ka nesanta wayar (phone) daga fuskarka. 


Idan zaka kalli bidiyo, ko zaka rubuta sako ko kuma zaka yi wani abu ka tabbatar ka nesanta waya daga fuskarka a kalla tsawon 40 cm. Saboda radiation dinta suna shiga cikin hancinka da bakinka su illata lafiyarka. Sannan kusantar da waya daga idanu na kashe karfin gani.


Karanta Wannan: Hanyoyi 3 dazaka gane inda wayar ka take bayan tabace ko ansace


5. Takaita Amfani da Bluetooth :


Inba ya zama dole ba ka takaita aiki da Bluetooth sannan kana gama amfani da shi to ka kashe. Bluetooth na amfani da Radiation da suke cutar lafiyar ciki sosai.6. Kada kayi amfani da waya (phone) idan tana chaji:


Amfani da waya a lokacin da take chaji na kashe karfin Battery sosai.


7. Ka Rage hasken wayarka (your phone) :


 A kowanne hali kada ka saki ka bar hasken wayar ka ya zama Full domin hasken na kashe lafiyar ido.


8. Kada Kadinga kure Volume:

Kure Volume shine abinda ke lalata sautin Speaker na waya.9. Kada kayi amfani da waya (phone) kana farawa barci 


 Amfani da waya kana farkawa bacci na illata kwakwalwa da Idanu. A kalla ka bari sai ka gama watsakewa sosai, son samu minti 40.10. Kada ka kwanta a kusa da waya (Phone) 


Radiation da waya ke samarwa yana da matukar illa sosai ga lafiya gangar jiki Musamman yayin da kake bacci. Don haka ka nesantar da wayarka daga inda kake bacci, san samu ka dinga ajewa nesa da gadonka.


Ananne zamu dakata sai kuma a darasi na gaba insha Allahu zamu cigaba daga inda muka tsaya, kar kumanta kuyi shiyarin domin wasu ma su karanta su amfana. 


Sannan kuma idan kanada tambaya ko kuma wani Karin haske game da Wannan Darasin namu sai kayi mana a comment, mukuma zamu maido maka da amsarka insha Allahu, kucigaba da kasancewa da wannan shafin namu wato Www.hausaweb.com.ng

1 Comments

  1. Live Dealer Casinos | Popular Games to Play, Reviewed
    You can find live dealer casinos on their web. But that's because their slots are not 해외 라이브 스코어 so 승인 전화 없는 토토 꽁 머니 easy to learn. A 아 샤벳 live dealer online 가상 화폐 란 casino is a great choice if you're looking for 벳플릭스 the

    ReplyDelete
Previous Post Next Post