Yadda Ake Fara Blogging-Bude Blog Cikin Sauki


Assalamu Alaikum Barka Da Zuwa Shafin Tips24 Wannan Blog Ne wanda Yake Koyarda Blogging A-Z

A darasinmu na Yau Zamu Koyi Yadda Ake fara Blogging Da Yadda Ake Bude Blog.
Abubuwanda Ke ciki:-

  • Zabar fanni
  • Zabat Sunan Blog
  • Bude Blog
Insha Allah Zamuyi Bayani Gameda wadannan Abubuwan Guda Uku nan saboda Sune Zasu Taimakeka Ka Mallaki Blog mai Dorewa Saboda Akan Samu Wasu Su Bude Blog Amma Su gagara Gina Shi Saboda Kuwa Ba a Gina Blog Din Akan Niche Ba Kawai Anyishi Kara Zube ne Shiyasa.

Yadda Ake Design Na Blogger Blog Cikin Sauki(Theme)

YADDA AKE ZABAR FANNI(NICHE) 

Kafin ka fara bloggin lallai kana bukatar ka zabi fanni wato abinda kafi Kwarewa akansa Saboda ka rika Rubuta Post naka a kansa Hakan Yakan Saka SEO naka Ya Zama Top Rank Saboda Ka Tsayawa Abu Daya,  Saboda Haka Saika Zabi akan Menene Zakayi blogging naka Akoi abubuwa irinsu Freebrowsing, Mobile Tricks,  Entertaiment, Girke girke, da Sauransu. 

YADDA AKE ZABAR SUNAN BLOG

Dole ya kasance ka Tsaida Sunan Blog Naka Sannan Sunan Blog Naka Ya Kasance Ya Dace da Sunan Niche Wato Fanninka (Sunan Blog naka Ya Zama Ya Dace da Abinda Kake Koyarwa a Blog Din). 

YADDA AKE BUDE BLOGGER


Sai ka Bi wadannan matakan Domin Mallakar Blog Naka:-

Dafarko Ka Bude Browser Naka Bayan Ka Bude Saika Rubuta Blogger.com


Saika Shiga Sign in Daga nan Zai Bukacu ka Cike Gmail Sa Password naka


Saika password naka bayan ka gama setup na Gmail Naka zai kaika inda zaka Bude new Blogger


Anan Zaka Saka TITLE wato taken Shafinka Wanda zai zama Shine Title naka saika Dannan NEXT


Anan zaka saka sunan blog naka kamar yadda kuke gani saika nemi sunan da wani bai rigaka ba saika danna NEXT


Anan kuma zaka saka sunan da kakeso ya fito a Profile naka wato wanda inkayi post zai fito saika Danna FINISH


 Congratulation ka kammala bude blog naka saura design


Dafatan Kowa ya gane in baka ganeba zaka iya Tambaya

Post a Comment

Previous Post Next Post