Yadda Zaku Bude Java Application Ko Game A Wayar Android


Assalamiu alaikum a yau insha Allah nazo mmuku da yadda ake Running na JAVA APP ko JAVA GAMES  a waya kirar cikin sauki.
Sanin kowa ne lallai java phone sun shigo Da fasaha kala kal hakan yasa suka shara a shekarun baya wanda Hakan Yasa Akayi musu Application masu kyau harda Games masu jan hankali.

Kada In cika mu da Surutu Bari muje kai tsaye Izawa ga Darasin namu akoi kafin gudanar da Wannan Aiki Lallai muna Bukatar Application na Android wanda zai Taimaka mana Wojen Aiwatarda Wannan Aiki.

Yadda Zaka Saita Edge Lighting A Wayarka Ta Android(Makeup)


Saboda haka ba tareda Bata Lokaci ba Ku shiga wannan Alamar ta Download Domin Saukarda Wannan Apk din.

DOWNLOAD JBED

Wannan Application din An Ginashi ne Domin Taimakawa Gurin bude java app a Wayar ta android Kamar dai yadda Kukasan Cewa ana Iya Bude Application na Android A Computer to haka ma Wannan Insha Allah zaka bude Java App da Games naka Dama Sauran programs din cikin sauki sannan Offline ne.

Zaka fara danna wannan alamar + din anan ne zai kaika cikin folder na wayarka inda anan ne zaka dauko application da kake son Run nashi Zaka iya dauko Java app a Irinsu Sefan.ru da sauransu.

 Daga nan saika danna Akan app naka zai Budu zaka iya kara girman screen a Setting


Na Tabbata wannan Application din zai taimaka Sosai Wojen Tunowa da wasu Java games da Apps irinsu 2go da dai sauran abinda sukayi fice musamman Lokacin Symbian.

Post a Comment

Previous Post Next Post